Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 19:42:33    
Za a jaddada tunanin kula da abubuwan da ke shafar rayuwar 'dan Adam a gun bikin bude taron wasannin Olympics na nakasassu

cri

Ran 21 ga wata da yamma a nan birnin Beijing, Mr. Fang Ming jagoran ayyukan kirkirar kide-kide na bikin bude taron wasannin Olympics na nakasassu na Beijing ya fayyace cewa, wannan biki mai ban tausayi da mutunci zai girgiza zukatan dukkan 'yan Adam.

Mr. Fang Ming ya nuna cewa, ba kamar tunanin bikin bude taron wasannin Olympics na Beijing ba, za a jaddada tunanin kula da abubuwan da ke shafar ruyuwar dan Adam a gun bikin bude taron wasannin Olympics na nakasassu, wasan kwaikwayo na bikin budewa zai girgiza zukatan dukkan 'yan Adam ta hanyar nuna mutunci. A sa'i daya kuma, wasan kwaikwayon da nakasassu za su yi zai zama salon musamma a gun bikin budewa.

Mr. Fang Ming ya fayyace cewa, kide-kiden bikin bude taron wasannin Olymipcs na nakasassu za su kasance kunshe da salon kasar Sin, kuma akwai salon zamani masu yawa.