Ran 21 ga wata a babbar cibiyar watsa labaru ta gasar Olympic ta Beijing, Mr. Chen Jian masanin al'amuran tattalin arziki kuma jagoran hukumar nazarin tattalin arzikin gasar Olympic ta Beijing ya nuna cewa, bayan gasar Olymics, tattalin arzikin birnin Beijing zai cigaba da bunkasuwa yadda ya kamata.
Mr. Chen Jian ya bayyana cewa, yayin da ake shirya gasar Olympic ta Beijing, tattalin arzikin birnin Beijing ya karu da kusan kashi 1 cikin kashi 100 a sakamakon gasar Olympic, kuma wannan ya sa kaimi ga ayyukan daidaita sana'o'i. Bayan gasar Olympic, tattalin arzikin birnin Beijing zai sami sabon karuwa, wannan zai warware matsalar raguwar yawan kudin da aka zuba.
Ban da haka kuma, ya kiyasta cewa, za a daidaita wasu sana'o'i bayan gasar Olympic ta Beijing, ciki har da sana'ar samar da gidaje da sha'anin gine-gine.
|