
Yau ranar 21 ga wata, an shiga kwana na 13 da soma gasar wasannin Olympics, za a fitar da lambobin zinariya 21 a wannan rana. Ya zuwa karfe 2 da minti 50 na yamma bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 5.

A gasar sassarfa ta kilomita 20 ta mata da aka shirya a ran nan da safe, 'yar wasa ta kasar Rasha Kaniskina Olga ta samu lambar zinariya.
A gasar iyo ta Marathon ta kilomita 10 ta maza, 'dan wasa na kasar Holand Van Der Weijden Maarten ya samu lambar zinariya.
A gasar karshe ta kwallon raga a filin rairayi ta mata biyu biyu, 'yan wasa na kasar Amurka wato Walsh Kerri da May-Treanor Misty sun samu lambar zinariya.

A gasar tseren kwale kwale na Multi-Hull Tornado, 'yan wasa na kasar Spain wato Echavarri Fernando da Paz Anton sun samu lambar zinariya.
A gasar tseren kwale kwale na Keel Boat Star, 'yan wasa na kasar Ingila wato Percy Iain da Simpson Andrew sun samu lambar zinariya.

Ban da su kuma, a ran nan da yamma da kuma da dare, za a fitar da lambobin zinariya 16 a gasannin dambe, da kwallon ruwa, da kwallon soft ball da dai sauransu.
Gasar keke da ke da kananan wiloli da ya kamata a yi a ranar 21 bisa shirin da aka tsara a da, an riga an dakatar da ita zuwa ranar 22 ga wata sakamakon ruwan sama.(Danladi)
|