Yau rana ce ta cikon kwanaki 100 da aukuwar girgizar kasa mai tsanani a gundumar Wenchuan ta kasar Sin, kuma jaridar people's daily ta kasar Sin ta yi sharhi.
Sharhin ya ce, a shekarar 2008, bi da bi ne aka samu girgizar kasa mai tsanani a gundumar Wenchuan da kuma shirya wasannin Olympics a birnin Beijing. Kwanaki 100 bayan aukuwar girgizar kasar, Beijing ta yi nasarar gudanar da wasannin Olympics ba tare da samun illoli daga girgizar kasar ba, haka kuma ba a ko yi kasala ba wajen gudanar da ayyukan agaji sakamakon wasannin Olympics.
Bayan haka, sharhin ya ce, yadda aka gudanar da ayyukan agaji, sai duniya ta sake fahimtar kasar Sin.
Sharhin ya kara da cewa, a ranar cikon kwanaki 100 da aukuwar girgizar kasa, muna nuna babban juyayi ga 'yan uwanmu da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon girgizar kasar.(Lubabatu)
|