
Bisa labari mai dumi dumi da muka samu, an ce, a cikin karon kusan karshe na wasan kwallon kafa na Olympics na Beijing da aka kammala ba da jimawa ba, kungiyar kasar Nijeriya ta lashe kungiyar kasar Belgium da ci hudu da daya. Sabo da haka, kungiyar kasar Nijeriya ta shiga karon karshe na wasan kwallon kafa na Olympics na Beijing, wanda za a yi a ran 23 ga wata da karfe 12 na rana bisa agogon Beijing.(Kande Gao)


|