Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 21:42:51    
Ingancin iskar Beijing yana cikin hali mafi kyau yanzu

cri

A ran 18 ga wata, Mr. Du Shaozhong, mataimakin direktan hukumar kiyaye muhalli ta Beijing ya bayyana wa manema labaru cewa, a cikin kwanaki 18 na watan Agusta da suka gabata, ingancin iskar Beijing na kowace rana dukkansu ya kai ma'auni mai kyau da aka tsara, kuma a cikin kwanaki 9 daga cikinsu, an samu ingancin iska mafi kyau, wato yawan kwanakin da suka samu ingancin iska mafi kyau ya kai kashi 50 cikin kashi dari bisa wadannan kwanakin da suka gabata. Mr. Du ya kara da cewa, yanzu ingancin iskar Beijing yana matsayi mafi kyau a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Du Shaozhong yana ganin cewa, a lokacin da ake samun yanayi maras kyau a cikin farkon kwanaki 10 na watan Agusta, dalilin da ya sa ingancin iskar Beijing ya iya kai ma'auni mai kyau shi ne ana aiwatar da matakan tabbatar da ingancin iskar Beijing da ake dauka domin gasar Olympic ta Beijing musamman kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)