Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 20:14:06    
An shiga kwana na goma na gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Yau ranar 18 ga wata, an shiga kwana na goma na gasar wasannin Olympics ta Beijing, gaba daya za a samu lambobin zinariya guda 18. Ya zuwa karfe 8 na yamma bisa agogon Beijing, an riga an samu lambobin zinariya guda 7.

A cikin gasar tseren mutum daya cikin wasanni 3 mata, 'yar wasa ta kasar Australia Emma Snowsill ta samu lambar zinariya.

A cikin wata gasar tseren kwale-kwale tsakanin maza biyu biyu, kungiyar 'yan wasan kasar Australia ta samu lambar zinariya. Haka kuma kasar Australia ta samu lambar zinariya a cikin wannan gasa ta mata.

A cikin gasar tseren keke ta mata a fili, 'yar wasa ta kasar Holland Marianne Vos ta zama zakara.

Ban da haka kuma, 'dan wasan kasar Sin Chen Yibing ya samu lambar zinariya a cikin gasar rings wato gasar zobe.

A cikin gasar uneven bars na mata, 'yar wasa ta kasar Sin He Kexin ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar tseren keke na bin juna kud da kud na maza a fili ta tsakanin kungiyar maza, kungiyar 'yan wasan kasar Birtaniya ta lashe kungiyar kasar Denmark ta samu lambar zinariya.