Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-17 18:52:14    
Sabunta: Gasar Olympic ta Beijing ta shiga kwana na 9

cri

Yau, wato ran 17 ga wata, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shiga kwana na 9. Ya zuwa karfe 5 da rabi na yamma, agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 14 a wannan rana.

Da misalin karfe 7 da rabi na safe, an soma gasar Marathon ta mata a filin Tian'anmen da ke cibiyar birnin Beijing. Daga karshe dai, Constantina Tomescu Dita daga kasar Romania ta samu lambar zinariya da awa 2 da minti 26 da dakika 44.

Haka kuma, a gun gasar karshe ta ninkayya cikin 'yanci ta mata ta zangon mita 50, Steffen Britta wadda ta zo kasar Jamus ta samu lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajinta na gasannin Olympic.

Sannan kuma a gun gasar karshe ta ninkayya cikin 'yanci ta maza ta zangon mita 1500, Mellouli Oussama na kasar Tunisiya ya samu wata lambar zinariya. Wannan ne lambar zinariya ta farko da kasar Tunisiya ta samu a gun gasar ninkayya ta wasannin Olympic.

A waje daya kuma, a gun gasar ba da sanda ta ninkayya ta mata 4 ta mita 400, kungiyar 'yan wasa ta mata ta kasar Australiya ta samu wata lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajinta na duniya.

Haka kuma, a gun gasar karshe ta ba da sanda ta ninkayya ta maza 4 ta mita 400, kungiyar 'yan wasan ninkayya na kasar Amurka da ke kunshe da Phelps Michael ta samu wata lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajinta na duniya da ta kafa a gun gasar Olympic ta Athens.

A gun wata gasar tseren kwale-kwale ta mata, kungiyar 'yan wasa ta kasar Britaniya ta samu wata lambar zinariya.

Kazalika kuma, a gun wata gasar harbe-harbe ta maza ta zangon mita 50, Qiu Jian na kasar Sin ya samu wata lambar zinariya.

A wannan rana da yamma, a gun gasar tseren kwale-kwale ta mata 4, kungiyar 'yan wasa ta kasar Sin ta samu wata lambar zinariya. Wannan ne karo na farko da 'yan wasa na kasar Sin sun samu lambar zinariya a gun gasar kwale-kwale ta mata 4.

Sannan a gun gasar karshe ta wasan badminton ta mata, Elena Dementieva daga kasar Rasha ta lashe Dinara Nafina, wata 'yar wasa daban ta kasar Rasha ta samu lambar zinariya.

Bugu da kari kuma, a gun gasar karshe ta wasan banminton ta mata biyu ta rukuni-rukuni, 'yan uwa na Williams ta kasar Amurka sun samu wata lambar zinariya.

Haka kuma, a gun wata gasar tseren kwale-kwale ta maza 4 marasa nauyi, kungiyar 'yan wasa ta Denmark ta samu wata lambar zinariya.

Kazalika, a gun wata gasar kwale-kwale da ake tuka shi da karfin iska, kungiyar 'yan wasa ta Britaniya ta samu wata lambar zinariya.

A waje daya kuma, a gun gasar tseren kwale-kwale na maza biyu, Pruchase Zac da Hunter Mark na kasar Britaniya sun samu lambar zinariya.

Daga karshe dai, a gun gasar wasan Judo ta mata mai nauyin kilo 63, Icho Kaori ta kasar Japan ta samu wata lambar zinariya. (Sanusi Chen)