Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-16 16:13:09    
An shiga kwana na takwas da soma gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Zhang Ning

Yau ranar 16 ga wata, an shiga kwana na takwas da soma gasar wasannin Olympics ta Beijing, za a fitar da lambobin zinariya guda 29 a duk ranar, wadda ta zama rana ta farko da ake fi fitar da lambobin zinariya a gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ya zuwa karfe 3 na yamma bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 7.

A gasar iyon rigingine ta mata ta mita 200, 'yar wasa ta kasar Zimbabuwei Coventry Kirsty ta samu lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajimtar duniya.

A gasar iyon da ake kira "Mallam-bude-littafi" ta maza ta mita 100, 'dan wasa na kasar Amurka Phelps Michael ya samu lambar zinariya, wannan ce lamba ta 7 da ya samu a gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A gasar iyo cikin 'yanci ta mata ta mita 800, 'yar wasa na kasar Ingila Adlington Rebecca mai shekaru 19 da haihuwa ta samu lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajimta na duniya.

A gasar sassarfa ta maza ta kilomita 20, 'dan wasa na kasar Rasha Borchin Valeriy ya samu lambar zinariya.

A gasar iyo cikin 'yanci ta maza ta mita 50, 'dan wasa na kasar Brazil Cielo Filho Cesar ya samu lambar zinariya.

A gasar harbi da bindiga da sauri ta maza ta mita 25. 'dan wasa na kasar Ukraine Petriv Oleksandr ya samu lambar zinariya.

A gasar kwallon badminton da ke tsakanin mace dai-dai, 'yar wasa ta kasar Sin Zhang Ning ta samu lambar zinariya.(Danladi)