|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-08-15 20:20:47
|
Hukumar wasannin Olympics ta duniya ta yabawa ayyukan shirye-shirye na wasannin Olympics na Beijing
cri
Ranar 15 ga wata, an shiga kwana na bakwai da aka soma gasar wasannin Olumpics na Beijing, kuma kusan rabin zangon gasar ya wuce, hukumar wasannin Olympics ta duniya ta gamsu da ayyukan share fage da na gudanarwa kan wasannin Olympics na Beijing.
A wannan rana, kakakin hukumar wasannin Olympics ta duniya madam Giselle Davies ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, hukumar na ganin cewa, kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya gudanar ayyukan shirye-shirye da kyau.
Mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympics Wang Wei ta ce, a hakika dai, ya zuwa yanzu, ana gudanar da wasannin Olympics na Beijing kamar yadda ya kamata, har ma shugaban hukumar wasannin Olympics ta duniya Jacques Rogge ya bayyana a wannan rana cewa, ba a bukatar cigaba da shirya taron daidaitawa da aka saba yi a 'yan kwanaki masu zuwa. (Bilkisu)
|
|
|