Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 20:18:04    
kauyen wasannin Olympics ya sami yabo daga wajen kwamitin wasannin Olympics na duniya da kuma 'yan wasa na kasashe daban daban

cri
Yau 15 ga wata, Madam Deng Yaping, mataimakiyar shugaban sashen kula da kauyen wasannin Olympics na kwamitin wasannin Olympics na Beijing, ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, tun bayan da aka fara wasannin Olympics a birnin Beijing, kauyen wasannin Olympics na gudana kamar yadda ya kamata, wanda kuma ya sami amincewa daga kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa da kuma 'yan wasa da jami'ai na kasashe daban daban. Tun bayan da aka bude kauyen wasannin Olympics, an gudanar da ayyuka daban daban ne bisa manufar "bauta wa 'yan wasa", don samar musu da gida mai kyau, ta yadda 'yan wasa na kasashe daban daban za su iya jin dadin zama a cikin kauyen da kuma samun kyawawan nasarori a gun wasanni.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, Jacques Rogge shi ma ya bayyana cewa, kauyen wasannin Olympics na Beijing ya zama kauyen wasannin Olympics mafi kyau. Jama'ar kasar Sin sun yi namijin kokari wajen gina kauyen, shi ya sa ya kamata su yi alhafari.(Lubabatu)