Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 20:09:48    
An shiga kwana na bakwai da soma gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
Yau ran 15 ga wata, an shiga kwana na bakwai da soma gasar Olympic ta Beijing. Ya zuwa karfe biyar da rabi na wannan rana da yamma, an fitar da lambobin zinariya 9, kuma an karya matsayin bajinta na wasan iyo guda uku.

A gun gasar wasan iyo na salon kwado na mata na zangon mita dari 2 da aka yi a ran 15 ga wata, Soni Rebecca, wata 'yar wasa ta kasar Amurka ta samu lambar zinariya da minti 2 da dakika 20 da 22, kuma ta karya matsayin bajinta na duniya.

A waje daya kuma, a gun gasar iyo ta salon riginginr ta maza ta zangon mita dari 2, Lochte Ryan, dan wasa na kasar Amurka ya samu wata lambar zinariya, kuma ya karya matsayin bajinta na duniya.

Bugu da kari kuma, a gun gasar wasan iyo da ke hade da salo iri iri na maza na zangon mita dari 2, Phelps Michael, wani sannanen dan wasa na kasar Amurka ya samu wata lambar zinariya, kuma ya karya matsayin bajinta na duniya. Sakamakon haka, ya zuwa yanzu, ya riga ya samu lambobin zinariya 6 a gun gasar Olympic ta Beijing, kuma ya karya matsayin bajinta har sau 6.

Haka kuma, a gun gasar karshe ta wasan daukan nauyi na ajin kilo 75 ta mata, 'yar wasan kasar Sin Cao Lei ta samun lambar zinariya, har ma ta karya matsayin bajinta na duniya. A gun gasar wasan iyo ta Freestyle ta mata ta zangon mita dari 1, Steffen Britta, 'yar wasa ta kasar Jamus ta samu lambar zinariya. Ayvazian Artur, dan wasa na kasar Ukraine ya samu lambar zinariya a gun gasar karshe ta harbe-harbe ta maza ta zangon mita 50. Liukin Nastia, 'yar wasa ta kasar Amurka ta samu lambar zinariya a gun gasar wasan lankwashe jiki ta mata. Tagwaye biyu daga kasar Slovakia Hochschorner Pavol, da Hochschorner Peter sun samu lambar zinariya a gasar kwale kwale na Canoe Slalom na maza biyu. 'Yar wasa Kaliska Elena daga wannan kasa ta zama zakara a gasar karshe ta kwale kwale na Kayak Slalom tsakanin mace dai dai.

Yau da yamma, za a ci gaba da fitar da sauran lambobin zinariya 9 a gun gasanni iri iri.