Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 20:06:00    
Zancen shugaban hadaddiyar kungiyar kula da harkokin harbe-harbe ta duniya kan haramta shan kwayoyi a wasan harbe-harbe

cri

Bisa labarin da wakiliyarmu ta ruwaito mana, an ce, yau Jumma'a, an sake samun lamarin shan kwayoyin kara kuzari a gun gasar wasannin Olympics a ake gudanarwa a nan Beijing. Dan wasan harbi da bindiga mai suna Kim Jong Su daga Korea ta Arewa ya zama dan wasa na farko da aka haramta masa lambar yabo da ya samu a gun gasar ta wannan gami saboda ya sha irin kwayar da ake kira " Propanolol". Mr.Olegario Rana, shugaban hadaddiyar kungiyar kula da harkokin harbe-harbe ta duniya ya fadi albarkacin bakinsa kan lamarin, inda ya furta cewa, wassu 'yan wasan harbi da bindiga ko kuma na kibiya sukan sha irin wannan kwaya da zummar kwantar da hankulansu yayin da suke yin gasa.

A lokaci guda, kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC ya shelanta cewa, an rigaya an kori yar wasan lankwashe jiki wato Gymnestics mai suna Do Thi Ngan Thuong ta Vietnam daga gun gasar wasannin yayin da wani 'yar wasan tseren keke mai suna Maria Morono daga kasar Spain ta bar nan Beijing saboda sun sha wassu haramtattun kwayoyi. ( Sani Wang )