Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 17:04:08    
An sake gano matsalolin shan maganin kara kuzari biyu daban a gun gasar Olympic ta Beijing

cri

A ran 15 ga wata, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya sanar da cewa, an sake gano matsalolin shan maganin kara kuzari biyu daban a gun gasar Olympic ta Beijing, wato Kim Jong Su, wani dan wasan harbi na kasar Koriya ta arewa da Do Thi Ngan, wata 'yar wasan lankwashe jiki ta kasar Viet Nam.

A gun wani taron manema labaru da aka yi a Beijing, madam Giselle Davis, kakakin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ta sanar da cewa, an riga an soke izinin shiga gasar Olympic ta Beijing na wadannan 'yan wasa biyu, kuma an riga an kore su daga gasar.

Madam Davis ta ce, a gun gasar karshe ta harbe-harbe ta maza ta zangon mita 10 da aka yi a ran 10 ga wata, Kim Jong Su ya samu wata lambar tagulla, sannan a gun gasar karshe ta harbe-harbe ta maza ta zangon mita 50, ya samu wata lambar azurfa. Yanzu an riga an dawo da wadannan lambobin yabo daga hannunsa. Kawancen harbe-harbe ta kasa da kasa ta tsai da kuduri cewa, an mika wa Jason Turner, wani dan wasa na kasar Amurka lambar tagulla ta gasar karshe ta harbe-harbe ta maza ta zangon mita 10. Kuma an mika wa Tan Zongliang, dan wasa na kasar Sin lambar azurfa ta gasar karshe ta harbe-harbe ta maza ta zangon mita 50, sannan kuma Vladimir Isakov, wani dan wasa na kasar Rasha ya samu lambar tagulla.

Madam Davis ta kuma sanar da cewa, Do Thi Ngan 'yar wasa ta kasar Viet Nam ta shiga gasar neman izinin cigaban da shiga gasar wasan lankwashe jiki ta mata da aka yi a ran 10 ga watan Agusta, kuma ta kai matsayi na 59. Yanzu an riga an soke izini da makin da ta samu. (Sanusi Chen)