Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 16:32:31    
Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gana da takwaran aikinsa na kasar Singapore Mr. S. R. Nathan

cri

A ran 15 ga wata, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gana da takwaran aikinsa na kasar Singapore Mr. S. R. Nathan da ya zo birnin Beijing don kallon gasar wasannin Olympic.

Shugaba Hu Jintao ya yi maraba da Mr. Nathan da ya zo kasar Sin don kallon gasar wasannin Olympic, ya nuna godiya ga bangaren kasar Singapore sabo da goyon baya da take yi, kuma yana fatan yan wasa na kasar Singapore za su samu sakamako mai kyau. Mr. Nathan ya bayyana cewa, bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing ya yi kyau karai da gaske, dukkan gasanni suna tafiya lami lafiya, mutanen kasa da kasa sun ji dadi a birnin Beijing. Wannan ya bayyana kirali na "'Duniya daya kuma buri daya", kuma ya bayyana ra'ayin raya duniya cikin jituwa da kasar Sin take bi. Kasar Sin ta samu nasarar shirya gasar wasannin Olympic, wannan ya zama alfahari ga duk matanen Asiya.

Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, a shekarun nan, dangantaka dake tsakanin Sin da Singapore tana bunkasa lami lafiya, shugabannin kasashen biyu su kan kai wa juna ziyara, ana samun sakamakon mai kyau wajen yin hadin gwiwa don samu moriyar juna a ko wane fanni, kuma a kan yi hadin gwiwa mai kyau a kan harkokin yankin da na duniya. Kasashen biyu suna dacewa da juna a fannin tattalin arziki, da zaman rayuwa, da dai sauransu, a halin yanzu, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da inganta hadin gwiwa, don samu bunkasuwa tare. Bangaren Sin yana son ya yi kokari tare da bangaren Singapore, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Singapore gaba da kuma kai wani sabon matsayi. (Zubairu)