Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-14 21:06:08    
(Sabunta) Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yabawa 'yan wasan kasar Sin

cri
A kwanakin nan, bi da bi ne manyan kafofin watsa labaru na kasar Afirka ta kudu suka yabawa 'yan wasan kasar Sin saboda lambobin da suka samu a cikin gasannin Olypmic na Beijing, kuma sun yaba wa jama'ar Sin da suka bayyana sha'awarsu kan gasannin wasannin Olympics.

Bayan da 'yar wasa ta kasar Sin Liu Zige ta samu lambar zinariya a gasar iyon da ake kira "Malam-bude-littafi" ta mita 200 ta mata a wasannin Olympics na Beijing, muhimman kafofin watsa labaru na kasar Australian sun bayar da labarai kan wannan cikin lokaci, inda suka yabawa kwarewar da 'yan wasa na kasar Sin ke nuna a gasar.

A wannan rana, "jaridar Cape Town" ta kasar Afirta ta kudu ta rubuta a shafi na farko da cewa, "'Yan wasan kasar Sin sun girgiza duniya!" A ran 13 ga wata, gidan TV na kamfanin rediyon kasar Afirka ta kudu ya yi sharhi kan kungiyar 'yan wasa mata ta kasar Sin wadda ta samu lambar zinariya ta gasar lankwashe jiki tsakanin kungiyoyin mata, ya ce, bayan kungiyar 'yan wasa maza ta kasar Sin ta samu lambar zinariya ta gasar lankwashe jiki tsakanin kungiyoyin maza a ran 12 ga wata, kungiyar 'yan wasa mata ta kasar Sin ta kafa wannan kyakkyawan sakamako a tarihi. "Kungiyar mata da ta maza gaba daya ne suka samu lambar zinariya ta gasar, wannan ba abin al'ajabi ba ne, shi ne hakikanin abin da ya faru a yanzu."

Babbar jaridar wasan motsa jiki ta kasar Faransa wato Jaridar L'equipe ta bayar da labari a ran 13 ga wata cewa, masu kallo na kasar Sin da ke halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing sun bayyana kyakkyawan hali. A cikin gasar lankwashe jiki, da 'yan wasa na kasashe daban daban suke yin gasa, sai 'yan kallo suka yi tafi raf-raf ga 'yan wasa, kuma sun yi shewa ga ko wane motsi da 'yan wasa suka yi.

Jaridar Nepszavai, wadda ta fi kawo tasiri a kasar Hungary, ta bayar da wani bayani a ranar 14 ga wata, inda aka nuna yabo sosai ga wasannin Olympics. A cikin bayanin an ce, a kwanaki 6 da suka wuce, an yi kamar kowa na kowa ke aiki kan wasannin a birnin Beijing da ke kunshe mutane sama da miliyan goma, sun shaida waa dukkan duniya cewa, kasar Sin wata babbar kasa ce mai ban mamaki. (Zainab)