Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-14 16:17:56    
An shirya bukukuwan nune-nune game da gasar wasannin Olympic sama da dari a birnin Beijing

cri
A ran 14 ga wata, mataimakiyar shugaban humukar kula da abubuwan gargajirya ta birnin Beijing madam Yu Pin ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, a lokacin da aka shirya gasar wasannin Olympic na Beijing, an shirya bubukuwan nune-nune game da gasar wasannin olympic sama da 110 a birnin Beijing, masu yawon shakatawa na gida da na waje dukkansu sun nuna yabo ga bubukuwan nan.

A gun taron manema labaru da aka shirya a cibiyar manema labaru na duniya na birnin Beijing na shekarar 2008 ran nan, madam Yu Pin ta bayyana cewa, a cikin bukukuwan wadansu sun bayyana kyakkywan al'adu da al'adar gargajiya na kasar Sin, wadansu kuma sun bayyana ra'ayin wasannin Olympic ga masu yawon shakatawa na gida da na ketare. Tun daga ran 1 zuwa ran 13 ga watan Agusta, nune-nune sun riga sun karbi masu yawon shakatawa na gida da na waje sama da miliyan guda da dubu 450, cikin har da masu yawon shakatawa na ketare da suka zo daga kasashe da yankuna kusan 60 da yawansu ya kai dubu 100.(Zubairu)