Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 17:30:28    
Ministan kudi na kasar Amirka Henry Paulson ya ba da lambar zinariya ta kiyaye muhalli ga kauyen wasannin Olympic na Beijing

cri
A ran 13 ga wata, ministan kudi na kasar Amirka Henry Paulson ya je kauyen wasannin Olympic na Beijing, inda ya wakilci kungiyar gina gine-gine masu kiyaye muhalli ta kasar Amirka, ya ba da lambar zinariya ta kiyaye muhalli ga kauyen wasannin Olympic na Beijing.

A gun bikin ba da lambar, shugabar kauyen wsannin Olympic na Beijing Chen Zhili ta ce, a lokacin da aka gina kauyen wasannin Olympic da sauran filayen wasannin Olympic na Beijing, an yi amfani da sabbin hikimomi da fasahohi da yawa na zaman domin kiyaye muhalli da tsima makamashi da kuma rage fitar da gurbataccen iska. Bugu da kari, an shirya wasannin Olympic bisa tunanin kiyaye muhalli da tsimin makamashi, kuma an sami sakamako mai kyau. An ba da lambar ga kauyen wasannin Olympic na Beijing, wannan ya tabbatar da sakamakon hadin kai da kasashen Sin da Amirka suka samu wajen amfani da fasahar dake kiyaye muhalli a cikin wasannin Olympic.

Mr. Paulson ya bayyana cewa, yin amfani da fasahar kiyaye muhalli, wannan zai mai da wasannin Olympic na Beijing ya zama wasannin Olympic da ya fi kiyaye muhalli.(Asabe)