Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 17:08:19    
Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya ji dadi sabo da gasar wasannin Olympic na Beijing tana gudana lami lafiya

cri
A ran 13 ga wata, daraktan zartaswa na kwamitin wasannin Olympic na duniya Mr. Gilbert Felli ya bayyana cewa, bayan an kimanta gasanni na kwanakin 5 da gasar wasannin Olympic na Beijing ke yi, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya ji dadi sosai sabo da gasar wasannin Olympic na Beijing tana tafiya lami lafiya a fannin gasanni, da hidima, da dai sauran fannoni.

Ran nan, a gun taron manema labaru da aka shirya a cibiyar watsa labaru ta gasar wasannin Olympic, Mr. Felli ya bayyana cewa, an ci nasarar shirya bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing, yan wasa na kasa da kasa dukkansu sun yaba wa kayayyaki da hidima sosai a kauyen wasannin Olympic, kuma sun ji dadin gasanni, da dakunan wasannin motsa jiki, da zirga-zirga, yan wasa na kasa da kasa suna nuna fiffikonsu da kwarewarsu a cikin gasanni, wannan ya shaida cewa gasar wasannin Olympic na Beijing tana tafiya lami lafiya. (Zubairu)