Bisa labarin da muka samu a ran 13 ga wata, an ce, ya zuwa karshen ranar 12 ga wata, akwai mutane fiye da miliyan 10 na kasar Sin sun lura da gasar Olympic ta "takardar Olympic ta salula".
Bayan kamfanin "China Mobile" ya zama abokin hadin gwiwa na gasar Olympic ta shekarar 2008 ta Beijing, kullum yana kokarin hada gasannin Olympic tare da oba-oba. A ran 1 ga watan Afrilu na shekarar da muke ciki, kamfanin "China Mobile" ya gabatar da "takardar Olympic ta salula" domin samar da labarai ga mutane daga dukkan fannoni.
|