Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 15:22:24    
An shiga kwana na biyar na gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Yau ranar 13 ga wata, an shiga kwana na biyar na gasar wasannin Olympics ta Beijing, gaba daya za a samu lambobin zinariya guda 17 a cikin gasannin da aka yi a yau. Ya zuwa tsakar rana, an riga an samu lambobin zinariya guda 6.

A ran 13 ga wata da safe, kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta mata ta kasar Sin ta lashe lambar zinariya wadda ta zama lambar zinariya ta farko da kasar Sin ta samu cikin wannan gasa a tarihi. Kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta kasar Amurka ta zama ta biyu. Kungiyar 'yan wasa na kasar Ramania ta zama na uku.

A gasar tseren keke kan tituna bisa tsawon lokaci, 'yar wasa ta kasar Amurka Armstrong Kristin ta samu lambar zinariya da mintoci 34 da dakika 51.72.

Phelps Micheal

A cikin gasannin iyo, 'yar wasa ta kasar Australia ta samu lambar zinariya ta gasar iyo mai salo daban-daban na mutun daya ta mata ta mita 200, kuma ta karya matsayin bajimtar duniya da ta taba samu da kanta. Dan wasan kasar Amurka Phelps Micheal ya samu lambar zinariya ta gasar iyon da ake kira "Mallam-bude-littafi" ta maza ta mita 200, kuma ya karya bajimtar duniya. 'yar wasan kasar Italiya Pellegrini Federica ta samu lambar zinariya cikin gasar iyon cikin 'yanci ta mata ta mita 200 tare da karya bajimtar duniya.

Ban da haka kuma, a cikin gasar iyon cikin 'yanci ta yada kanin wani ta maza ta mita 200 na mutane hudu-hudu, kungiyar 'yan wasan kasar Amurka ta samu lambar zinariya da mintoci 6 da dakika 58.56, kuma ta karya bajimtar duniya.