Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 21:37:42    
Majalisar gudanarwa ta Sin ta tabbatar da sana'ar yawon shakatawa a matsayin babbar sana'a dake jagorantar ayyukan sake gina lardin Sichuan bayan bala'in girgizar kasa

cri

' Majalisar gudanarwa ta Sin ta riga ta tabbatar da sana'ar yawon shakatawa a matsayin babbar sana'a dake jagorantar ayyukan sake gina lardin Sichuan bayan bala'in girgizar kasa, da kara zuba jari, da kyautata ingancin gine-ginen yawon shakatawa da kuma sa kaimi ga wassu kamfanoni wajen bunkata sana'ar yawon bude ido', kamar yadda mataimakin shugaban babbar hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin Mr. Wang Zhifa ya bayyana yau Talata a nan birnin Beijing.

Sa'annan Mr. Wang ya bayyana cewa, kamfanonin yawon shakatawa na lardin Sichuan sun yi hasarar da ta kai kudin Sin Yuan biliyan 46 da miliyan 500 sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa. Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fito da jerin manufofin nuna gatanci don farfado da wuraren yawon shakatawa da kuma kyautata matsayin bada hidima.

Kazalika, Mr. Wang ya sa ran farfado da dukkan wuraren yawon shakatawa na lardin Sichuan bayan shekaru uku. ( Sani Wang )