Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 19:30:50    
Kafofin yada labarai na ketare sun yaba wa gasar wasannin Olympics da ake gudanarwa a nan Beijing

cri

An bude gasar wasannin Olympics ta karo na 29 cikin gagarumin hali a ran 8 ga wata a nan birnin Beijing. Kwanakin baya a jere, kafofin yada labarai na ketare sun bayar da labarai da yawa kan gagarumar gasar, inda suka buga babban take gare ta.

Jaridar da ake kira "Tribune" ta kasar Kamaru dake matsayin gwamnatin kasar ta bayar da wani bayani jiya Litinin a kan cewa, daidai ta bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing ne, kasar Sin ta aike da sakon nuna aminci da shimfida zaman lafiya da kuma na samun jituwa ga duk fadin duniya.

Jaridar da ake kira " Lianhe Zaobao" ta kasar Singapore ta bayar da bayanai da dama a 'yan kwanakin baya, inda ta buga babban take ga gaar wasannin Olympics ta Beijing yayin da take tabbatar da cewa wannan gagarumar gasa za ta samar wa kasar Sin dimbin kayayyakin gado da ba na wasan motsa jiki ba.

Ban da wannan kuma, jaridar da ake kira " Japan China News" da ake bugawa cikin harshen Sinanci da Japananci ta buga wani bayanin edita don yaba wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing; Bayanin editan ya kuma ce, karin karfin da kasar Sin ta samu daga dukkan fannoni da kuma kara yin tasiri da take yi a duniya sun kasance tushe da kuma tabbaci ne ga gudanar da wannan gasa mai kayatarwa cikin nasara.

Kazalika, jaridun kasashen Rasha da Vietnam da kuma Uraguay sun bayar da labarai don jinjina wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing. ( Sani Wang )