Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 16:18:24    
An shiga kwana na huku na gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Yau ranar 12 ga wata, an shiga kwana na hudu na gasar wasannin Olympics ta Beijing, gaba daya za a samu lambobin zinariya guda 19. a cikin gasannin da aka yi a yau. Ya zuwa tsakar rana, an riga an samu lambobin zinariya guda 6. A ran 11 ga wata, an samu lambobin zinariya guda 13.

A ran 12 ga wata da safe, kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta kasar Sin ta lashe lambar zinariya wadda ta taba rasa kafin shekaru 4. Kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta kasar Japan wadda ta taba samu lambar zinariya a gasar Olympic ta Athens ta zama na biyu. 'kungiyar 'yan wasa na kasar Amurka ta zama na uku.

A gun gasar iyo cikin 'yanci na tsawon mita 200 na maza, 'dan wasa na kasar Amurka Phelps na kasar Amurka ya samu lambar zinariya, kuma ya karya matsayin bajimtar duniya. Wannan lambar zinariya ta uku da ya samu a gasar Olympic ta Beijing.

A cikin gasar iyon kwado ta mata ta mita 100, 'yar wasan kasar Australia Jones Leisel ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar wasan iyon rigingine ta maza ta mita 100, 'dan wasan kasar Amurka Peirsol Aaron ya samu lambar zinariya tare da karya bajimtar duniya.

A cikin gasar wasan iyon rigingine ta mata ta mita 100, 'yar wasa ta kasar Amurka Coughlin Natalie ta samu lambar zinariya.

Ban da haka kuma, 'dan wasan kasar Korea ta kudu Jin Jong Oh ya samu lambar zinariya a gasar harben sannu a hankali da karamin bindiga na mita 50 na maza. Tsohon 'dan wasan kasar Sin Tan Zongliang ya sami lambar tagulla.