Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 14:28:49    
Masu sauraron CRI sun yabawa wasannin Olympic na Beijing

cri

Bayan da aka bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, masu sauraron gidan rediyon kasar Sin, wato CRI sun buga waya domin nuna babban yabo ga kyawawan shirye-shirye da aka yi a bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma suna fatan za a gudanar da wasannin Olympic yadda ya kamata.

Bayan kallon gagarumin bikin bude gasar, Pompillu Andrei, mai sauraro na harshen Romania na CRI ya aiko wani sakon E-mail ga sashen Romania, inda ya bayyana cewa, bi da bi ne kasar Sin take cika alkawarin da ta yi wa kasashen duniya, kuma wasannin Olympic na Beijing zai kasance babban nasara bisa matsayin duniya da za a rubuta cikin tarihi.

Dawod Jabar Khel, mai sauraro da ke yankin Peshawar a kasar Pakistan ya buga waya cewa,wasannin Olympic na Beijing yana ta mika yanayin zaman lafiya da farin ciki da dorewa. Bikin bude wasannin Olympic na Beijing ya yi kamar wata salla. Yana jin farin ciki kwarai, kuma yana fatan alheri ga wasannin Olympic na Beijing. Ba ma kawai kasar Sin za ta samu girmamawar wasannin Olympic ba, hatta ma duk kasashen Asiya za su samu gaba daya.

Zia Bumia, mataimakin shugaban cibiyar watsa labarun duniya ta kasar Afghanistan ya buga waya ga CRI cewa, kasar Sin ta kira gasar wasannin Olympic ta Beijing a madadin duk kasashen Asiya. An kammala duk ayyukan share fage bisa babban matsayi. Wannan gasar za ta zama dandalin zaman lafiya da shawarwari. Duk jama'ar kasar Afghanistan suna fatan alheri da za a gudanar da wasannin Olympic na Beijing yadda ya kamata. (Fatima)