Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 17:12:47    
Yau an shiga kwana na uku wajen gudanar da gasar Olympic ta Beijing

cri
Yau, wato ran 11 ga wata, an shiga kwana na uku wajen gudanar da gasar Olympic ta Beijing. Ya zuwa karfe 2 da rabi na wannan rana da yamma, agogon Beijing, an riga an samu lambobin zinariya 5 a gasannin ninkayya da harbe-harbe biyu.

A wannan rana da safe, kungiyar 'yan wasan ninkayya maza ta kasar Amurka ta samu lambar zinariya a gun gasar wasan tseren ninkayya na mita dari-dari na 'yan wasa 4 , kuma an yanke matsayin bajinta na duniya.

A waje daya kuma, a gun gasar ninkayya ta mita dari 1, Mr. Kitajima Kosuke, sarkin ninkaya na kasar Japan ya samu wata lambar zinariya, kuma ya yanke matsayin bajinta.

Sannan kuma Bindra Abhinav, dan wasan harbi na kasar Indiya ya samu wata lambar zinariya a gun gasar harbi ta maza ta mita 10. Wannan ne lambar zinariya ta farko da kasar Indiya ta samu a gun gasar Olympic.

Bugu da kari kuma, madam Trickett Lisbeth, 'yar wasan ninkayya ta kasar Australiya ta samu wata zinariya a gun gasar wasan ninkayya ta malam-bude-littafi ta mita dari 1 a gun gasar Olympic ta Beijing. Sannan Adlington Rebecca, 'yar wasan ninkayya ta kasar Britaniya ta samu wata lambar zinariya ta mita dari 4.

Ban da wannan, a ran 11 ga wata, kwamitin Olympic na kasa da kasa ya sanar da cewa, an gano maganin EPO, wani maganin sa kuzari daga jikin Moreno Maria, wata 'yar wasan tseren keke ta kasar Spain. Sakamakon haka, an kori Moreno Maria daga gasar Olympic ta Beijing. (Sanusi Chen)