Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 14:02:40    
Batun fashewar boma-bomai a Xinjiang ba zai jawo illa ga wasannin Olympic ba, a cewar jami'in kwamtin shirya wasannin Olympic na Beijing

cri
Ran 10 ga wata a birnin Beijing, Mr Wang Wei,mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing kuma babban sakatare ya bayyana cewa, batun ta da boma-bomai da aka yi ran nan da sassafe a jihar Xinjiang ba zai jawo illa ga wasannin Olympic na Beijing ba.

Mr Wang ya bayyana cewa, ran 10 ga wata da misalin karfe 2 da rabi da safiya, masu yin laifuffuka sun kai farmaki ga wani ofishin 'yan sanda da ke Kuche a jihar Xinjiang ta hanyar yin amfani da motar texi, bugu da kari kuma sun kai farmaki ga hukumar masana'antu da cinikayya a wurin. Kuma sun lalata motocin 'yan sanda 2. Yayin da suka bude wuta, 'yan sanda 2 da mai tsaro daya sun ji rauni, kuma an lalata dakuna da dama. Amma wannan ba zai jawo illa ga wasannin Olympic na Beijing ba. A sa'i daya kasar Sin za ta kara tabbatar da matakan tsaron yankunan da abin ya shafa.

Kuma Mr Wang ya nuna cewa, wannan ba shi da alaka da wasannin Olympic.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, yanzu an riga an warware batun ta'addanci mai ta da hankali. 'Yan sanda sun karbe 'yan ta'ada 8, kuma sun kama 'yan ta'ada 2. Dayan 2 sun mutu domin fashewar boma bomai da kansu. Yanzu 'yan sanda suna cigaba da neman kama 'yan ta'ada 2 da suka tsere, kuma za su gudanar da aikin yi musu tuhuma tun da wuri.(Fatima)