Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 13:56:29    
Dai Bingguo ya gana da shugaban kwamitin kungiyar AU Mr. Jean Ping

cri
A ran 10 ga wata, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Mr.Dai Bingguo ya gana da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika, wato AU Mr. Jean Ping dake zo birnin Beijing don halartar bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing.

Mr. Dai Bingguo ya nuna yabo ga halin da Afrika da dangantakar dake tsakanin Afrika da kasar Sin suke ciki, kuma ya bayyana cewa, kasar Sin ta mai da hankali a kan muhimmiyar rawa da kungiyar AU ke takawa wajen harkokin yankin da na duniya, kasar Sin tana son ta ci gaba da yin kokari tare da kasashen Afrika da kungiyar AU, don ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika gaba.

Mr. Jean Ping ya taya murnar samun nasarar shirya bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing. Ya bayyana cewa, yanzu, dangantakar dake tsakanin Afrika da Sin tana bunkasa lami lafiya, kasashen Afrika da jama'arsu suna jin dadin haka. Kungiyar AU tana son ta kara yin cundaya da kasar Sin a fannin siyasa, don sa kaimi ga hadin gwiwa da bangarorin biyu suka yi yanzu. (Zubairu)