Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 13:54:33    
Firaminista Wen Jiabao ya gana da shugaban kasar Amurka Bush da sauran shugabannin kasashen waje

cri
A ran 10 ga wata, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya gana da shugaban kasar Amurka Mr. Bush da sauran shugabannin kasashen waje da suka zo birnin Beijing don halartar bikin bude gasar wasannin Olympic bi da bi.

Lokacin da ya gana da shugaba Bush, Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa, yana fatan tattalin arzikin kasar Amurka ya kara karuwa, kuma darajar kudin dalar Amukar ta samu ingantuwa lami lafiya, yana fatan bangaren Amurka ya yawaita yawan kayayyakin fasaha na zamani da za a sayar wa kasar Sin, ya kuma amince da matsayin Sin na tattalin arzikin kasuwanci. Ya bayyana cewa, ya kamata bangarorin Sin da Amurka su yi kokari tare, don yin rigakafin yaduwar kariyar ciniki, da kara daidaita tsarin tattalin arziki a manyan fannoni, da kuma yin cudanya a fannin cinikayya na duniya. Mr. Bush ya bayyana cewa, bangaren Amurka yana fatan ya kara yin shawarwari cikin hadin gwiwa da kasar Sin, shi kansa zai ci gaba da yin kokarin wajen sa kaimi ga aikin raya dangantakar hadin gwiwa mai zurfi tsakanin kasar Amurka da Sin.

Lokacin da ya gana da firaministan kasar Guinea Mr. Souare, firaminista Wen Jiabao ya bayyana cewa, ya kamata bangarorin biyu su yi kokari wajen aiwatar da nasarorin da aka samu a taron koli na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka shirya a birnin Beijing. Mr. Souare ya ce, kasar Guinea tana son ta karfafa hadin gwiwa da take yi da kasar Sin.

Ban da wannan kuma, firaminista Wen Jiabao ya gana da firaministan gwamnatin wucin gadi na kasar Fiji, da firaministan kasar Tonga, da na kasar Vanuatu, da na kasar Finland, da na kasar Netherlands, da na Albania, da kuma tsohon firaministan kasar Jamus bi da bi. (Zubairu)