Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 10:48:19    
An shiga kwana na uku na gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Xian Dongmei

Yau ranar 11 ga wata, an shiga kwana na uku na gasar wasannin Olympics ta Beijing, gaba daya za a samu lambobin zinariya guda 13. a cikin gasannin da aka yi a ran 10, an samu lambobin zinariya guda 14.

A ran 11 ga wata, 'yan wasa na kasar Sin za su yi kokari domin samun lambobi na

A cikin gasannin da aka yi a ran 10, 'dan wasan iyo na kasar Amurka Michael Phelps ya karya matsayin bajimta na duniya kuma ya samu lambar zinariya a gasar iyo mai salo daban-daban na mita 400 na maza da mintoci 4 da dakika 3.84.

A gun gasar mai salo daban-daban na mita 400 na mata, 'yar wasa ta kasar Australiya Stephanie Rice ta karya matsayin bajimta na duniya kuma ta samu lambar zinariya da mintoci 4 da dakika 29.45.

A gun gasar iyo cikin 'yanci na yada kanin wani na tsawon mita dari-dari na mata hudu-hudu, kungiyar kasar Holland ta samu lambar zinariya da mintoci 3 da dakika 33.76 a yau da safe.

Haka kuma 'dan wasan iyo na kasar Korea ta kudu Park Taehwan ya samu lambar zinariya da mintoci 3 da dakika 41.86 a gun gasar iyo cikin 'yanci na mita 400 na maza. 'Dan wasan iyo na kasar Sin Zhang Lin ya samu lambar azurfa a gasar, wadda ta zama lamba ta farko da 'yan wasa maza na kasar Sin suka samu a gun gasannin iyo na wasannin Olympics.

A gasar harbe-harben fistole na mita 10 na mata, 'yar wasa ta kasar Sin Guo Wenjun ta samu lambar zinariya da zobba 492.3.

A cikin gasar taka tsalle cikin ruwa mai katako na tsayin mita uku na mata, 'yan wasa na kasar Sin Guo Jingjing da Wu Minxia sun samu lambar zinariya.

A gun gasar harbe harben bindiga daga fannoni daban-daban na maza, 'dan wasa na kasar Czech Kostelecky David ya samu lambar zinariya.

A gun gasar daukan nauyi na ajin kilo 53, 'yar wasa ta kasar Thailand P. Jaroenrattanatarakoon ta samu lambar zinariya. A gun tseren keke kan hanyar mota ta mata, 'yar kasar Ingila Nicole Cooke ta samu lambar zinariya.

A gun gasar harba kibiya da aka shirya a ran 10 ga wata, kungiyar mata ta kasar Korea ta kudu ta samu lambar zinariya, kungiyar mata ta kasar Sin ta zo ta biyu a gun gasar.

A gasar judo ta mata ta ajin kilo 52, 'yar wasa ta kasar Sin Xian Dongmei ta samu lambar zinariya.

A gasar judo ta maza ta ajin kilo 66, 'dan wasa na kasar Japan Uchishiba Masato ya samu lambar zinariya.

A gasar wasan takobi mai nauyi, wato "Epee", 'dan wasa na kasar Italiya Tagliariol Matteo ya samu lambar zinariya.