Ran 9 ga wata, an yi zagaye na karshe na gasar wasan daukan nauyi na ajin kilo 48 na mata ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 a dakin wasan motsa jiki na jami'ar koyon ilmin sararin sama ta Beijing, a karshe dai, 'yar wasa daga kasar Sin Chen Xiexia wadda ke da shekaru 25 na haihuwa ta samu zama ta farko bisa sakamako na karshe na kilo 212, wannan ne lambar zinari ta farko da kungiyar wakilan wasannin Olympic ta kasar Sin ta samu a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma ta karya matsayin bajimta na gasar wasannin Olympic ta wannan wasa.
"yar wasa daga kasar Turkey Ozkan Sibel ta samu lambar yabo ta azufa, kuma 'yar wasa daga birnin Taibei na kasar Sin Chen Weiling ta samu lambar yabo ta tagulla a bayansu. (Jamila Zhou)
|