Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:23:42    
An kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Beijing da ta zo na farko a fannoni da dama a tarihin wasannin Olympics

cri

Yau wato ran 8 ga wata da karfe 8 da yamma bisa gogon birnin Beijing, an kaddamar da gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta karo na 29 a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, wadda ta zo na farko a fannoni da dama a tarihin wasannin Olympics. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Jacques Rogge ya yi jawabi a gun bikin bude gasar, kuma shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sanar da kaddamar da gasar.

Kungiyoyin 'yan wasa na dukkan kasashe membobi 204 na babban iyalin Olympics sun riga sun iso birnin Beijing da kuma halartar bikin bude gasar da aka yi a yau da dare, haka kuma shugabanni fiye da 80 na kasashe daban daban ciki har da shugaba Bush na Amurka da firayim minista Fukuda Yasuo na Japan da shugaba Sarkozy na Faransa da da shugaban majalisar dattijai na kasar Nijeriya David Mark da shugaban majalisar wakilai ta Nijeriya Dimeji Bankole da kuma minitsan wasannin motsa jiki na kasar Nijer Seydou su ma sun halarci bikin. Bisa kidayar da gwamnatin kasar Sin ta bayar, an ce, yawan 'yan wasa da suka shiga wannan gasar ya zarce dubu 11 yayin da yawan manema labarai masu halartar gasar ya kai fiye da dubu 30. Wadannan jimlolin da muka ambata a baya sun karya matsayin bajimta na wasannin Olympics da bikin bude wasannin Olympics.

A cikin jawabin da Mr. Rogge ya yi, ya nuna godiya ga kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing wato BOCOG da kuma dimbin mutane masu aikin sa kai, kuma ya yi kira ga 'yan wasa da su shiga gasanni bisa burin zama zakaru da sada zumunci da girmama ruhun Olympics. Haka kuma a madadin BOCOG, shugaban kwamitin Liu Qi ya yi marhabin da zuwan baki daga kasashe daban daban, da kuma nuna godiya ga abokai da suka nuna kulawa da goyon baya ga gasar wasannin Olympics.

A gun bikin bude gasar, an nuna wasan fasaha mai taken "kyakkyawan Olympic" na tsawon kimanin awa guda, wanda sanannen darekta na kasar Sin Zhang Yimou ya zama babban darekta. Bisa bayanin da Zhang Yimou ya yi, an ce, an yi kokari don neman hada abubuwan al'adun gargajiya na kasar Sin da ruhun Olympics tare, da kuma mika wa duniya hasshen "sada zumunci da samun jituwa".

Lokacin da ake kusantar kawo karshen bikin, shahararren dan wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe na kasar Sin Li Ning da ya taba samu lambobin zinariya 3 a gun gasar wasannin Olympics ta Los Angeles a shekara 1984 ya kunna babbar wutar yola ta wannan gasar wasannin Olympics.(Kande Gao)