Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 18:01:08    
Za a kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Beijing a yau da dare wadda ta zo na farko a fannoni da dama a tarihin wasannin Olympics

cri
Yau wato ran 8 ga wata da karfe 8 da yamma bisa gogon birnin Beijing, za a kaddamar da gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta karo na 29 a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, wadda ta zo na farko a fannoni da dama a tarihin wasannin Olympics. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Jacques Rogge zai yi jawabi a gun bikin bude gasar, kuma shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai sanar da kaddamar da gasar.

Kungiyoyin 'yan wasa na dukkan kasashe membobi 205 na babban iyalin Olympics sun riga sun iso birnin Beijing, kuma za su halarci bikin bude gasar da za a yi a yau da dare, haka kuma shugabanni da muhimman kusoshi fiye da 80 na kasashe daban daban ciki har da shugaba Bush na Amurka da firayim minista Fukuda Yasuo na Japan da shugaba Sarkozy na Faransa da shugaban majalisar dattijai na kasar Nijeriya David Mark da shugaban majalisar wakilai ta Nijeriya Dimeji Bankole da kuma minitsan wasannin motsa jiki na kasar Nijer Seydou su ma za su halarci bikin. Bisa kidayar da gwamnatin kasar Sin ta bayar, an ce, yawan 'yan wasa da za su shiga gasar ya zarce dubu 11 yayin da yawan manema labarai masu halartar gasar ya kai fiye da dubu 30. Wadannan jimlolin da muka ambata a baya sun karya matsayin bajimta na wasannin Olympics da bikin bude wasannin Olympics.

A gun bikin bude gasar, za a nuna wasan fasaha mai taken "kyakkyawan Olympic", wanda sanannen darekta na kasar Sin Zhang Yimou ya zama babban darekta. Bisa bayanin da Zhang Yimou ya yi, an ce, za a yi kokari don neman hada abubuwan al'adun gargajiya na kasar Sin da ruhun Olympics tare, da kuma mika wa duniya hasshen "sada zumunci da samun jituwa".

Wannan shi ne karo na farko da aka shirya wasannin Olympics a kasar Sin da aka fi samun yawan mutane a ciki, kuma wannan shi ne karo na uku da aka shirya wasannin Olympics a birane na kasashen Asiya. Za a sa aya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing a ran 24 ga wata. (Kande Gao)