Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 17:40:43    
Hu Jintao ya kira gagarumar liyafa domin marabtar zuwan baki masu martaba da za su halarci wasannin Olympic na 29

cri
Ran 8 ga wata da tsakar rana a cikin dakin liyafa na dakin taruwar jama'a a birnin Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kira gagarumin liyafa domin marabtar zuwan baki masu martaba da za su halarci wasannin Olympic a karo na 29.

Shugaba Hu ya ba da jawabinsa a gun liyafar maraba, inda ya nuna godiyarsa ga duk wanda ya ba da gudummowa ga wasannin Olympic na Beijing.

A cikin lokacin neman samun damar gudanar da wasannin Olympic da na share fage, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun samun taimako da yawa daga gwamnatoci da jama'a na kasashen duniya, kuma sun samu goyon baya daga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa da babban iyalin wasannn Olympic. Yanzu a nan ina muku godiya, kuma ina fatan za ku isar da godiyata ga duk wanda ya ba da gudummowa ga wasannin Olympic na Beijing.

Shugaba Hu ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic gagarumar gasa ce ta motsa jiki, kuma dandalin ne kan musanyar al'adu. Wasannin Olympic na duniya sun tattara mutane na kasashe daban da kabilu daban da al'adu daban a gu daya, ta yadda za a zurfafa fahimta da dangantakar abokantaka na jama'ar kasashen duk duniya, kuma wasannin Olympic sun ba da gudummowa masu dimbin yawa ga sha'anin tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa na dan Adam.

Shugaba Hu ya furta cewa, yanzu dai kasashen duniya suna fuskanta zarafin bunkasuwa da ba a taba fuskanta ba, kuma suna fuskanta kalubale mafi tsanani. Yanzu kasashen duniya sun fi bukatar fahimtar juna da hakuri da juna da kuma hakin gwiwa tare da juna. Wasannin Olympic na Beijing ba ma kawai damar kasar ba, hatta ma damar duniya ce.

Kamata ya yi mu ta da tunani Olympic na hada kai da sada zumunta da zaman lafiya ta hanyar halartar gasar wasannin Olympc, domin sa kaimi ga jama'ar kasashen duniya da su zurfafa fahimtar juna da kara sada zumunta da cika gibin da ke tsakaninsu, ta yadda za a ciyar da aikin kafa wata duniya mai zaman lafiya har abada cikin annashuwa gaba.

Shugaba Hu ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2001 da aka cimma nasarar neman samun damar gudanar da wasannin Olympic, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun cika alkawarin da suka yi wa kasashen duniya yadda ya kamata. Sun tsaya tsayin daka kan hasashen Olympic na kyautata muhalli da kimiyya da fasaha da zaman takewar al'adu, kuma sun yi namijin kokari kan ayyukan share fage a duk fannoni. Ya yi imani cewa, a karkashin goyon baya na kwamitin wasannin Olympic da babban iyalin wasannin Olympic, dole ne za a gudanar da wasannin Olympic na Beijing mai alama bisa babban matsayi.(Fatima)