Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 17:32:53    
Mr. Wen Jiabao ya gana da wasu shugabannin kasashen waje da za su halarci bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
A yau da safe a birnin Beijing, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da firayim ministocin kasashen Australia, da Djibouti, da Tailand, da Myanmar, da Chadi, da kuma Rasha wadanda za su halarci bikin bude gasar wasannin Olympic, inda ya yi maraba da su, kuma sun musaya ra'ayoyinsu a kan dangantakar dake tsakanin bangarori biyu da batutuwan dake jawo hankulansu.

A lokacin da ya gana da firayim ministan kasar Djibouti Dileita Mohamed Dileita, Mr. Wen Jiabao ya ce, bangaren Sin zai ci gaba da ba da taimako ga bangaren Djibouti wajen bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman jama'ar kasa. Mr. Dileita ya bayyana cewa, kasar Djibouti za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan nuna goyon baya ga jama'ar kasar Sin.

A lokacin da ya gana da firayim ministan kasar Chadi Youssouf Saleh Abbas, Mr. Wen Jiabao ya ce, bangaren Sin ya nuna goyon baya ga gwamnatin Kasar Chadi da ta yi kokarin aiki wajen kikaye kwanciyar hankalin kasar da ciyar da bunkasuwar tattalin arziki gaba. Mr. Abbas ya nuna cewa, da akwai zumunci mai zurfi a tsakanin gwamnati da jama'ar kasar Chadi da kasar Sin, yana fatan kasar Chadi za ta kara yin aikin hadin gwiwa iri daban daban da kasar Sin.(Asabe)