Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 16:55:06    
Wasu manyan jami'an siyasa na kasashen waje sun yi imani cewa za a cimma nasarar wasannin Olympic

cri
Ran 7 ga wata, wasu manyan jami'an siyasa na kasashen waje da shugabannin kungiyoyin duniya sun bayyana cewa, sun yi imani cewa za a cimma nasarar wasannin Olympic na Beijing.

Kafin bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing, Mr Javier Solana, babban wakilin kula da manufofin tsaro da harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai ya aika da wasikar taya murna ga Mr Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin, inda yana fatan alheri da za a cimma nasarar wasannin Olympic na Beijing. Mr Javier Solana ya bayyana cewa, kungiyar tarayyar Turai ta yabawa kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi wajen share fagen wasannin Olympic. Ya yi imani cewa, wasannin Olympic na Beijing, sun kasance wani sabon masomi ne na inganta dangantakar abokantakar sada zumunta tsakanin kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai, kuma bangarorin biyu za su fuskanci kalubale mafi yawa tare da juna a cikin lokaci mai zuwa.

Yayin da Mr Fukuda Yasuo, firayin ministan kasar Japan yake zantawa da manema labaru na kasar Sin a rubutacce, ya jaddada cewa, shekarar bana shekara ce ta wasannin Olympic na Beijing ga kasar Sin, kuma shekara ce ta cika shekaru 30 da a bude kofa ga kasashen waje. Ya bayyana cewa, yana sanya ran cewa wasannin Olympic za su kasance dandalin shaida fata da karfi na kasar Sin wajen ba da gudummowa ga zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa na kasar Sin da na duk duniya.

Yayin da shugaba Kalkot Mataskelekele na kasar Vanuatu, wanda ke share fagen halartar bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, yana sa ran cewa gasar wasannin Olympic na Beijing za ta zama gasar wasannin Olympic mafi cimma nasara a cikin tarihi.

Kuma Mr Murat Basesgioglu, ministan harkokin gida na kasar Turkey da Mr Ivan Vacjunic, mataimakin shugaban kasar Ukraine da Mr Traian Basescu, mataimakin babban sakataren kungiyar MDD suna fatan alhari da za a cimma nasarar wasannin Olympic na Beijing. (Fatima)