Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 16:50:45    
An samo nasarar aikin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing

cri
A ran 8 ga wata, Mr. Wang Wei, mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing, ya bayyana cewa, an samo nasarar aikin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing, kuma an shiga lokacin yin gasar wasannin Olympic.

A gun taron manema labaru da aka shirya a babbar cibiyar kafofin watsa labaru na gasar wasannin Olympic na Beijing, Mr. Wang Wei ya bayyana cewa, yau muhimmiyar rana ce ga birnin Beijing, har ma ga duk kasar Sin. Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing ya riga ya yi aikin shirya a fannin masu aikin sa kai da wuraren shiryar gasar wasannin olympic, birnin Beijing ya riga ya yi shiri sosai, don maraba da abokai daga ko ina.

Kazalika kuma, Mr. Wang Wei ya ce, akwai shugabannin kasashe da gwamnatoci, da membobin sarauta kusan 90 za su halarci bikin dudewa da za a shirya a ran nan da dare. (Zubairu)