Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 16:46:48    
Shugaba Hu Jintao ya gana da shugabanin kasashen waje da suka zo don halartar bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing

cri
A ran 8 ga wata na safe, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gana da wadansu shugabanin kasashen waje da suka zo don halartar bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing bi da bi.

Lokacin da ya gana da shugaban kasar Afghanistan Mr. Hamid Karzai, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, bangaren Sin ya nuna girmamawa ga ikon mulkin kasar Afghanistan, da cikakkan yankin kasar, da kuma 'yancin kan kasar, ya nuna girmamawa ga hanyar raya kasa da bangaren Afghanistan ya zaba. Bangaren Sin yana son ya ba da taimako da dukkan kokarinsa ga aikin farfado na kasar Afghanistan.

Lokacin da ya gana da shugaban kasar Romaniya Mr. Traian Basescu, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, shekara mai zuwa ita ce shekarar cika shekaru 60 da kasashen biyu suka kafa dangantakar diplomasiyya, yana fatan bangarorin biyu za su iya yin amfani da wannan, don ciyar da dangantakar abokantaka da yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasar Romaniya gaba, da kuma kai sabon matsayi.

Lokacin da shugaba Hu Jintao ya gana da shugaban kasar Isra'ila Mr. Shimon Peres, ya bayyana cewa, kasashen Sin da Isra'ila su nuna girmamawa juna, kuma taimakon juna, an samu babbar nasara wajen yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, yana fatan bangarorin biyu za su iya ci gaba da yin cudanya a dukkan fannoni, da kuma yawaita hadin gwiwa da aka yi don samu moriyar juna.

Lokacin da ya gana da shugaban kasar Croatia Mr. Stjepan Mesic, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, bangaren Sin ya nuna girmamawa ga hanyar raya kasa da jama'ar kasar Croatia suka zabi bisa halin da suka ciki, da kokari da suka yi don shiga yunkurin hada da kasashen Turai a gaba daya. (Zubairu)