Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 13:37:34    
Jacques Rogge ya nuna babban yabo ga wasannin Olympic na Beijing

cri
Ran 7 ga wata, a gun taron manema labaru da aka shirya a babbar cibiyar labaru na wasannin Olympic, Mr Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya ya bayyana cewa, wasannin Olympic za su ciyar da bunkasuwar kasar Sin gaba kuma kasashen duniya za su kara fahimtar kasar Sin.

Mr Jacques Rogge ya bayyana cewa, wasannin Olympic na Beijing zai gabatar da kasar Sin mai kyakkyawan hali da kuma al'adun kasar Sin na tsawon shekaru 5000 ga jama'ar duk duniya, wannan zai daidaita ra'ayin da kasashen duniya suka dauka kan kasar Sin, kuma wannan ne na da muhimmanci sosai ga sauran jama'ar kasashen duniya.

Mr Jacques Rogge ya nuna babban yabo ga aikin shirye shirye na wasannin Olympic na Beijing, kuma ya yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi a fannin kiyaye muhalli da sauransu. Ya furta cewa, ya zuwa yanzu, an riga an samu babban sakamako wajen kyautata matsalar gurbataccen muhalli. Yanzu yanayin Beijing yana cikin hali mai kyau ga 'yan wasa.(Fatima)