Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 12:55:39    
Hu Jintao da matarsa sun yi marhabin da manyan bakin da suka yi rajistar halartar gasar Olympic ta Beijing

cri
A ran 8 ga wata da rana a babban dakin taron jama'a na Beijing, shugaban kasar Sin Hu Jintao da matarsa Liu Yongqing sun yi marhabin da manyan bakin da suka yi rajistar halartar gasar Olympic ta karo na 29.

Bayan bikin marhabinsu, shugaba Hu Jintao ya shirya musu gagarumin liyafa a dakin liyafa na babban dakin taron jama'ar kasar Sin domin nuna marhabin da manyan bakin da suka zo daga kasashe da yankuna daban daban na duk duniya.

Bisa al'adar kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, shugabanni da firayin ministoci na kasashe daban daban za su halarci bikin kaddamar da gasar Olympic a matsayin manyan bakin da suka yi rajista bisa gayyatar da kwamitocin wasannin Olympic na kasashensu suka yi musu. Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayar da labari cewa, manyan 'yan siyasa fiye da 80 za su halarci bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing da sauran bukukuwan da abin ya shafa a matsayin bakin da suka yi rajista. (Sanusi Chen)