Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-07 14:46:35    
An fara mika wutar gasar wasannin Olympic a karkarar birnin Beijing

cri

Bayan an kammala mika wutar gasar wasannin Olympic a birnin a rana ta farko, a ran 7 ga wata, aikin mika wutar a yankin birnin Beijing ya shiga kwana na biyu, an fara mika wutar a karkarar birnin, mutane masu mika wutar su 268 za su mika wutar da yawan tsawon hanyar zai kai kusan kilomita 15.

Da karfe 7 na safe, an shirya bikin fara mika wutar a filin Wongcheng dake gundumar Yanqing, mai gwajin zirga-zirgan jirgin sama Mr. Li Zhonghua ya zama mai mika wutar na farko. Wutar gasar wasannin Olympic za ta kai Babbar Ganuwar kasar Sin dake yankin Badaling da dai sauran wurare masu yawon shakatawa a karkarar birnin, kuma za a mika wutar a kogin Dayunhe dake Tongzhou.

Wadda samu lambar yabo ta zinari a gasar wasannin Olympic ta Sydney Liu Xuan, da wanda ya samu lambar yabo ta zinari a cikin gasanin wasannin Olympic guda uku Alejandrina Mireya Luis Hernandez, da mai lambar yabo ta zinari a gasar wasannin Olympic ta Athens Yang Wenjun, da dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Morocco Hicham El Guerrouj da dai sauransu za su shiga aikin mika wutar.

Wutar gasar wasannin Olympic za ta kai wurin yawon shakatawa na Ditan a ran nan da karfe 6 da minti 35 da yamma, mai mika wutar na karshe, kuma zibiya Song Zuying za ta kunna wuta a cikin tukunyar wutar gasar wasannin Olympics. (Zubairu)