Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-06 14:37:31    
Bi da bi ne, tawagogin wakilai na kasa da kasa suka iso birnin Beijing

cri

A ran 5 ga wata, bi da bi ne, tawagogin wakilai na kasa da kasa da za su halarci gasar wasannin Olympics ta Beijing suka iso filin jirgin sama na birnin Beijing, haka kuma bi da bi ne, suka shiga cikin kyauyen wasannin Olympics.

Da karfe 5 na safe na ranar 5 ga wata, 'yan wasa na karo na farko na tawagar wakilai ta kasar Afghanistan da kuma malamai masu horar da su sun iso filin jirgin sama na birnin Beijing.

Ban da su kuma, a ran nan da safe, tawagogin wakilai na kasar Laos, da Nepal, da Serbia sun iso birnin Beijing.

A tsakiyar rana kuma, tawagar wakilai ta kasar Philippines ta iso birnin Beijing.

A ran nan da yamma kuma, tawagar wakilai ta kasar Vietnam ta iso birnin Beijing, sa'an nan kuma ta shiga cikin kauyen wasannin Olympics.

Ban da tawagar wakilai ta kasar Vietnam kuma, tawagar kasar Tanzaniya ta iso birnin Beijing a ranar 5 ga wata da yamma. Shugaban tawagar wakilai ta kasar Tanzaniya Mr. George Mkuchika ya ce, kasashen Sin da Tanzaniya suna da dankon zumunci, kasar Sin ta taimakawa kasar Tanzaniya sosai a fannonin wasanni.(Danladi)