Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-05 21:32:33    
Tawagar wasannin Olympic ta Tanzaniya ta isa birnin Beijing

cri
Ran 5 ga watan Agusta da misalin karfe 3 da yamma, tawagar wasannin Olympic ta kasar Tanzaniya ta isa birnin Beijing.

A wannan lokaci gaba daya tawagar Tanzaniya ta tura 'yan wasa guda 10 domin halartar gasanni, a ciki da akwai 'yan wasan guje guje da tsalle tsalle 8 da 'yan wasan iyo 2. Yayin da shugaban tawagar wasannin Olympic ta kasar Tanzaniya ke zantawa da wakilimmu, ya bayyana cewa, kasashen Sin da Tanzaniya suna da dankon zumunci, kasar Sin ta ba da gudummowa mai dimbin yawa ga sha'anin motsa jiki na kasar Tanzaniya. A sa'i daya kuma ya furta cewa, 'yan wasan Tanzaniya su kan sami kyakkyawan sakamako a cikin gasannin guje guje da tsalle tsalle, ana fatan 'yan wasan kasar Tanzaniya za su sami sakamako mai kyau a cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Fatima)