 An kammala aikin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Chengdu na lardin Sichuan. A ran 5 ga wata da yamma, an kai wutar yola ta gasar wasannin Olympic zuwa birnin Beijing.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ran 6 ga wata da safe, za a fara mika wutar yola ta wasannin Olympic daga kofar Wu ta gidan sarautar kasar Sin, kuma za a shafe kwananki 3 ana mika wutar a Beijing. Tsawon hanyar mika wuta a birnin Beijing ya kai kilomita 38.92, gaba daya za a dauki tsawon awa 8 da minti 54, kuma masu mika wuta 841 za su halarci aikin mika wutar yola. Mr. Yang Liwei, dan sama jannati na farko na kasar Sin zai zama mai mika wuta na farko a birnin Beijing. (Fatima)
|