Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-05 16:10:16    
An mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Chengdu a lardin Sichuan

cri

A ran 5 ga wata da safe, an mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Chengdu, babban birni na lardin Sichuan a kudu maso yammancin kasar Sin. Wannan shi ne zango na karshe na mika wutar a lardin Sichuan.

Da karfe 8 da minti 10 na safe, an yi bikin fara mika wutar wasannin Olympics na zangon Chengdu a filin kera kayayyakin da ake fitarwa na Chengdu, kuma masu mika wutar 315 sun bi hanya mai tsawon kilomita 13.02, kuma an kammala mika wutar a cibiyar nune-nune ta kasa da kasa. Zhang Shan ta zama mai mika wutar ta farko, wadda ita ce zakarar wasannin Olympics kuma mutumiyar lardin Sichuan. Mai mika wutar na karshe shi ne Yu Zhirong, wakilin rundunar sojojin kasa da ke aiki a sama kuma shugaba na wata rundunar sojojin kasa da ke aiki a sama na yankin sojoji na Chengdu.

Daga ran 6 zuwa ran 8 ga wannan wata, za a mika wutar a Beijing wadda ta zama zango na karshe na mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Zainab)