Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-04 21:00:06    
Tawagar wasannin Olympic ta Tanzaniya ta tashi zuwa Beijing

cri
Tawagar wasannin Olympic ta kasar Tanzaniya ta riga ta tashi zuwa birnin Beijing a ran 4 ga wata domin halartar gasar wasannin Olympic ta Beijing da za a bude a ran 8 ga watan Agusta.

Ran 3 ga wata, kwamitin wasannin Olympic na kasar Tanzaniya ya kira gagarumin biki ga 'yan wasa 10 na kasar Tanzaniya da za su halarci gasanni a birnin Beijing da sauran membobin tawagar. Mr George Mkuchika, ministan ma'aikatar motsa jiki da al'adu da sako na kasar Tanzaniya ya mika tutar kasa ga Mr Fabian Joseph, dan wasan guje guje da tsalle tsalle kuma mai rike da tuta na tawagar Olympic ta kasar Tanzaniya. Mr George Mkuchika ya isar da fatan alheri na shugaba Jakaya Kikwete na kasar Tanzaniya cewa, gwamnatin kasar Tanzaniya da jama'arta suna nuna musu goyon baya, kuma suna fatan za su samu lambar gasar wasannin Olympic(Fatima)