A kwanakin abya, jaridar "New Vision" ta kasar Uganda ta bayar da bayanin edita kan shafin farko cewa, wasannin Olympics na Beijing zai zama wani abin al'ajabi na duniya.
An ce, idan ake cikin birnin Beijing, ana iya jin niyya ta kasar Sin wadda ke da yawan mutane biliyan 1.3, wannan al'ummar wadda ta taba gina babbar ganuwa ta riga ta karbar kalubane na gudanar da wasannin Olympics.
A cikin wannan bayani, an ce, ana iya ganin ma'aikata masu shirya wasannin Olympics suna yin kokari na karshe kan ko wane titi, mutane masu aikin sa kai dubu 10 suna yin murmushi, suna yin musanya tare da baki na kasashen waje cikin harsuna dabam daban. Kuma an kammala ayyukan gina dakuna da filayen wasannin Olympics dabam daban, an yi amfani da fasahohi mafi cigaba kan fannonnin wasanni da sadarwa daga fannoni dabam daban. Dukkansu za su kawatar da dukkan 'yan wasa kwarai.
|