Yau ranar 4 ga wata ya rage sauran kwanaki 4 za a soma gasar wasannin Olympics ta Beijing, kakakin gwamnatin birnin Beijing Mr. Liu Zhi ya bayyana a ran nan cewa, birnin Beijing ya shirya sosai a fannoni daban daban, birnin Beijing yana da kwarewa sosai wajen shirya gasar wasannin Olympics cikin nasara.
A gun wani taron manema labaru da aka shirya a cibiyar watsa labarai ta duniya da ke birnin Beijing, Mr. Liu ya gabatar da cewa, tun daga ranar 20 ga watan jiya, birnin Beijing ya fara gudanar da tsarin zirga zirgar motoci masu lambobin mara da masu lambobin cika da dai sauran matakai, haka kuma ya kaddamar da sababbin hanyoyin jiragen kasa masu zirga-zirga da yawansu ya kai uku, da kuma hanyoyin motocin bas musamman don na Olympics da yawansu ya kai 34, domin tabbatar da zirga zirga yadda ya kamata a yayin da ake shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing. Birnin Beijing yana da gadaje dubu 665 wajen biyan bukatun 'yan yawon shakatawa da suka zo daga kasashen waje. Ban da wannan kuma, birnin Beijing ya shirya sosai a fannonin makamashi, da ingancin abinci, da ba da hidimar likitanci da dai sauransu, musamman ma ingancin iska ta Beijing ya riga ya kai wani matsayi yadda ya kamata a cikin wani mako.(Danladi)
|