Jiya 31 ga watan Yuli, jakadan kasar Sin a Mauritius, Mr.Gao Yuchen ya kira liyafa, don yin ban kwana da shugaban kasar Mauritius Anerood Jugnauth, da kuma matarsa, wadanda za su tashi zuwa birnin Beijing don halartar bikin bude wasannin Olympics.
Mr.Jugnauth ya nuna babban yabo a kan huldar aminci da hadin gwiwa da ke ta bunkasa a tsakanin kasarsa da Sin. Ya ce, duk duniya na zura ido a kan wasannin Olympics na Beijng. Ya nuna yabo a kan babban kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka yi wajen share fagen wasannin Olympics, kuma yana da imanin cewa, wasannin Olympics na Beijing zai kasance wasannin da ya fi samun nasara kuma kasaita a tarihi.(Lubabatu)
|