|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-08-01 22:06:40
|
Kasar Sin ta shirya sosai wajen ba da hidimar yanayi a lokacin wasannin Olympics
cri
A ranar 1 ga wata, kakakin watsa labarai na hukumar yanayi ta kasar Sin Yu Xinwen ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, hukumar yanayi ta kasar Sin ta shirya sosai wajen ba da hidimar yanayi a lokacin wasannin Olympics, ciki har da daukar matakai son canza yanayi.
Amma, a waje daya kuma ya bayyana cewa, hanyar daukar matakai don canza yanayi tana kan matsayin gwaje-gwaje, saboda haka, tana iya ba da amfani kan yanayi mara tsanani kawai, ba za ta kawo tasiri sosai ga yanayi mai tsanani ba. (Bilkisu)
|
|
|